![eboostr exclude list editor eboostr exclude list editor](https://cdn1.iconfinder.com/data/icons/photo-editor-line/32/exclude_photo_editor-512.png)
![eboostr exclude list editor eboostr exclude list editor](https://fivethirtyeight.com/wp-content/uploads/2021/12/2021-CHESS-CHAMPS-1205-16x9-1.png)
Malam ya fara bada labarin baba suda a takaice wanda shi kuma shine ya ba yara labarin rigingimun dankane, kuma ni a fahimta ta malam ya nusar damu ne cewa tara yara da basu labaru wata hanyace ta tarbiya, kamar yadda Allah ta'ala ya dauki wannan salo a kaso mai girma na Alkur’ni kamar : suratu Yusufa kacokam dinta ta bada labarin annanbi yusufa ne, ta kuma bada mahimmanci kan al’amuran zamantakewa ,wasu surori kuma annabi Isa, Musa, Dauda da Sulaiman, Ibrahin da sauransu, da labarin sarakuna kamar Fir’auna da Lamarudu, duk wannan domin mu dau izna. Mun kasance muna kishirwan mawallafa irin malam Kabiru ruwan wankin daudar zamantakewa, don kuwa mun kosa da masu kwashe baiwar talifi da Allah ta’ala ya musu sui ta yawo tsakanin so da ki, da soyaiya da kiyaiya kamar mu hausawa wata al’umma ce wacca bata da wata matsala sai soyaiya.
![eboostr exclude list editor eboostr exclude list editor](https://m.media-amazon.com/images/I/41a79naVGSL._SL500_.jpg)
Shekaran jiya nake karanta shi lokacinda na bakonci dangina a omdurman na jamhuriyar sudan, amma lokaci zuwa lokaci sai in kyalkyale da dariya saboda in nayi hakuri a taran aradu da kan dankani wani lokaci to wani lokacin kuma bazan iya hana bakina ‘yancin dariya ba. ĭuk wannan takaitaccen yabon ba wai nasan shi bane, saidai na kwatanta zakakurancinsa ne sakamakon karanta littafinsa mai suna ‘’suda’’ littafinda ya hada nishadantarwa da tarbiya da azanci. Malam Kabiru Yakasai ba shakka haziki ne mai matukar hikima, da alama kuwa hannunsa ya jima yana goga alkalami kan takarda.